Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Ma’Aikata a Afrika ta Kudu

Ma'aikatan gwamnati na zanga-zanga a harabar asibitin Natalaspruit da ke birnin Johannesburg don neman karin albashi, ran 18 ga Agusta, bayan da gamayyar kungiyoyin ma'aikata ta ki tayin karin albashin da gwamnati ta yi mata.

Ma’aikatan kasar Afrika ta Kudu sun fara yajin aiki a yau bayan sun wancakalar da wani tayin karin albashin da gwamnatin kasar ta yi mu su.

Ma’aikatan kasar ATK sun fara yajin aiki a yau laraba kamar yadda sui ka shirya yi, bayan sun wancakalar da wani tayin karin albashin da gwamnatin kasar ta yi mu su. Kawancen kungiyoyin da ke wakiltar ma’aikata miliyan daya da dubu dari ukkun da su ka hada da malaman makarantu da likitoci da ‘yan sanda da sauran ma’aikatan gwamnati, ya ce za a ci gaba da yajin aiki har sai an samu biyan bukata. Ma’aikatan na neman lallai sai a yi mu su karin albashi da kashi 8 da digo 6 cikin dari da kuma karin kudaden tallafin samun gidan zama.

Dubban ma'aikatan gwamnati sun yi jerin gwano zuwa Majalisar Dokoki a birnin Cape Town lokacin zanga-zangarsu ta kwana guda na neman karin albashi.
Dubban ma'aikatan gwamnati sun yi jerin gwano zuwa Majalisar Dokoki a birnin Cape Town lokacin zanga-zangarsu ta kwana guda na neman karin albashi.

Gwamnatin kasar ta yi tayin kara albashi da kashi 7 cikin dari sannan kuma ta ce za ta kara yawan kudaden tallafin samun gidan zama daga dola 87 zuwa dola 95 a wata, wato daga kwatankwacin Naira dubu 13 da 50 zuwa Naira dubu 14 da 250, ko kuma daga Cfa jikka 43 da rabi zuwa jikka 47 da dala 10.

XS
SM
MD
LG