Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata ‘Yan Najeriya, su Hada Kai


Masu zanga-zanga rike da alluna dake dauke da sakonni ga gwamnatin Najeriya, May 31, 2014.
Masu zanga-zanga rike da alluna dake dauke da sakonni ga gwamnatin Najeriya, May 31, 2014.

Anyi zanga-zangar lumana a gaban ofishin jakadanshin Najeriya dake birnin Washington, D.C.

Kungiyar jama’ar arewacin Najeriya a nan Amurka wato Zumunta, reshen Washington, D.C. da Maryland da kuma Virginia ta gudanar da zanga-zanga lumana a gaban ofishin jakadanshin Najeriya dake birnin Washington, DC.

Kungiyar tayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan nemo daliban Chibok da aka sace su a makarantarsu ta sakandare a watan da ya wuce.

Shugaban kungiyar Auwal Babanliya, yace yakamata ‘yan Najeriya, su hada kai domin idan ba’a hada kai ba za’a cimma buri dakile masu tada kayar bay aba.

Mai shekaru saba’in da uku Mr. Dewa, bai gamsu da abubuwan dake faruwa a Najeriya bay ace” abunda ya fito dani shine abunda ya faru a Chibok, wani addini yace a kwashe ‘yan mata aje a siyardasu babu wani addini a duniya, Obangiji bai yardaba.”

Wata ‘yar asalin garin Gwoza dake jihar Borno Miss. Angelina, tafadi ra’ayinta dangane da rashin tsaro da ya addabi arewa maso gabashin Najeriya, tace"bamu iyayin barci bamu san abunda ake ciki ba tunda aka sace ‘yan mata bamu samu kwanciyar hankali ba."
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG