Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Jahilci A Kano


Wata daliba a arewacin Nijeriya, na kokarin yakar jahilci
Wata daliba a arewacin Nijeriya, na kokarin yakar jahilci

Ana samun cigaba a yaki da jahilcin da ake yi a jihar Kano; to amma akwai wasu matsaloli nan da can.

An sami cigaba a yaki da jahilci a jihar Kano; amma har yanzu akwai kalubale sosai. A 1990 ne aka kafa makarantar yaki da jahilci a Kano kuma tun sannan mutane sama da miliyan biyu ne su ka amfana; sannan kuma akwai azuzuwa sama da 7,000 a fadin Kano.

Shugabar Cibiyar Yaki Da Jahilci a Kano Furfesa Fatima Umar ta ce sun a fama da kalubale iri iri; to amma mafi tsanai shi ne rashin halartar makaranta da maza ke yi. Ta ce musamman lokacin damuna maza bas u halartar makaranta sabo da zuwa gona. Ta ce a wurare da dama sun mai da makaranta da yamma saboda maza su rinka samun damar zuwa makarantar.

Wani manomi mai suna malam Shehu Ibrahim Sa’idu Rano, wanda ya amfana da makarantar ta yaki da jahilci y ace ya koyi rubuta sunansa da sunayen iyayensa da rubuta lambobi da kuma zayyana watanni da kwanaki; kuma ya iya kidaya daya zuwa goma da turanci. Shi kuwa wani yaro mai suna Ibrahim Isma’il ya ce rashin zuwansa makarantar ya janyo masa ci-baya da yawa. Ya ce dan abin da ya samu daga makarantar Islamiyya ya ke amfana.

Wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ce kimanin ‘yan Nijeriya 35 cikin dari basu iya karatu da rubutu ba, wanda hakan ya sa kwararru ke ganin Nijeriya fan a fuskantar babbar matsala ta cigaba. Shi kuwa shugaban Hukumar Yaki da Jahilci na kasa baki daya Alhaji Yusuf Paiko y ace daya daga cikin manyan matsalolin shi ne kasa biya malamai daga bangaren jihohi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG