Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Sari-Ka-Boke Na Bukatar Dabara Dabam Da Wadda Ake Amfani Da Ita


Janar Abdurrahman Dambazau yace tilasdokar-ta-baci ta samar da hanyar da jama'a zasu iya bi su gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata ba wai su zauna cikin wahala kawai ba

Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Abdurrahman Bello Dambazau, yace tilas duk matakan da gwamnatin Najeriya zata dauka na shawo kai ko murkushe 'yan Boko Haram da sauran masu aikata laifi a kasa, su zamo matakai ne da a karkashinsu za a mutunta hakkin jama'a na gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum ba tare da zullumi ba.

Janar Dambazau mai ritaya, ya fadawa VOA Hausa a cikin wata hira ta musamman cewa kafa runduna ta 7 ta sojojin da aka yi a Maiduguri, ba ita ce zata shawo kan lamarin ba, domin kuwa fadan sari-ka-noke ake fuskanta, ba wai yaki ne na gaba da gaba da abokin gabar da ka san inda yake kuma kana ganinsa ba.

Yace babban matakin da ya kamata gwamnati ta dauka game da mayakan Boko Haram, shine kasafta su daki-daki domin zabtare karfinsu, ta hanyar gano wadanda aka sanya su daukar makamai bisa dole, da wadanda suka shiga a saboda jahilci, da wadanda suke ciki a sa boda talauci, da kuma ainihin wadanda suke yi domin akida.

Janar Dambazau yace kowane daya daga cikin wannan nau'i na mayakan, hanyar takalarsa dabam ce, idan ana son samun nasara.

Ga cikakken bayanin da Janar din yayi...

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG