Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Masallaci A Konduga


Jami’an tsaro sun ce an kasha mutane 44 cikin masallacin, yayin da aka kashe wasu farar hula 12 a wani harin dabam a kauyen Ngom a kan hanyar ta Konduga

Wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar nan ce ta Boko Haram sun bindige suka kasha mutane 44 dake sallah a cikin wani masallaci a garin Konduga, kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Jami’an tsaro sun ce an kasha wasu fararen hula su 12 a wani harin dabam da aka kai duk a lokaci guda.

Wannan farmaki na jiya lahadi na daya daga cikin hare-haren da aka dora laifin kais u a kan kungiyar Boko Haram mai ikirarin cewa tana son kafa daular Musulunci ne a yankin.

Ba a san dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram zata kai hari a kan Musulmi dake ibada ba, koda yake a can baya ta sha kai farmaki a kan masallatan da malamansu suka yi tur da akidar tsageranci irin ta Boko Haram, haka ma shugabanta Abubakar Shekau, ya fada cikin wani faifan bidiyo cewa zasu kai farmaki a kan duk Musulmin da a ganinsu bay a goyon bayansu.

An kai harin na Konduga ne da safiyar lahadi. Wani jami’in tsaro da kuma wani dan kungiyar banga masu farautar Boko Haram, sun fadawa kamfanin dillancin labaran AP a yau litinin cewa sun kidaya gawarwakin mutanen da suka mutu a cikin masallacin.

Usman Musa na kungiyar bangar ta “Civilian JTF” y ace an kasha ‘ya;yan kungiyartsu 4 a lokacin da suka isa garin na Konduga, suka yi artabu da abinda ya kira “’yan ta’adda dauke da muggan makamai.”

Musa yace maharani sun a sanye da rigunan sojojin Najeriya, wadanda watakila sun sace ne a daya daga cikin hare-haren da suka kai kan sansanonin sojan Najeriya.
A kan hanyarsu ta komowa daga Konduga, jami’an tsaron sun taras da wani wurin da aka kai ma hari dabam a wani kauye mai suna Ngom, kilomita 5 daga Maiduguri, inda Musa yace ya kirga gawarwaki 12 na fararen hula.

26 daga cikin masallatan da aka kai ma hari a garin Konduga sun a kwance sun a jinya yanzu haka a asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
XS
SM
MD
LG