Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Ofishin 'Yan Sanda A Garin Gumau


Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012.
Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012.

Jami'ai a karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi sun ce babu wanda ya mutu, amma mutum guda ya ji rauni a sanadin wannan harin

Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun bude wuta a kan ofishin 'yan sanda na garin Gumau dake yankin karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Jami'ai a karamar hukumar da kuma mutanen garin na Gumau, sun ce wannan lamarin ya faru daidai lokacin sallar Isha'i jiya laraba, a lokacin da 'yan bindigar su akalla biyu a kan babur suka tsaya suka bude wuta kan ofishin 'yan sandan.

Babu wanda ya mutu, amma an ji rauni wa mutum guda wanda a yanzu haka yake asibiti.

Wani mazaunin garin na Gumau, ya fadawa Muryar Amurka cewa 'yan bindigar sun isa a kan babur, sai suka sauka suka doshi ofishin 'yan sanda, inda aka ji karar harbe-harbe. Ba a samu wani labari na abinda ya samu 'yan bindigar ba.

Shugaban karamar hukumar ta Toro, yayi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu, su kuma kasance masu sanya idanu a koyaushe, tare da kai rahoton duk wani abinda ba su yarda da shi ba ga hukiuma.

Har yanzu hukumomin 'yan sanda a Jihar Bauchi ba su yi bayani game da wannan harin ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG