Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kai Hari Cibiyar Horas Da Yan Sanda A Pakistan


Wasu yan bindiga da suka boye fuskokinsu sun kai hari a cibiyar horar da yan sandan Pakistan a kudu maso gabashin birnin Quetta, a jiya Litinin kuma sun kashe kuratan ‘yansanda sama da 40 da wani jami’insu, sun kuma raunata mutane sun fi dari.

Rahottani sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane da dama da ba a san adadinsu ba. Daga baya rundunar sojin Pakistan suka zagaye makarantar, inda fada ya kaure a tsakaninsu har zuwa asubahin yau Talata.

Wadanda suka shedi al’amarin sun ce sun jiashewa masu yawa da tashin bama bamai sau biyu a cikin cibiyar dake da dakunan kwanan yan sandan da ake horarwa.

Rahotannin farko na nuna akwai mutane sama da dari biyu a cikin ginin lokacinda aka fara rigimar.

Fira ministan Pakistan Nawaz Sharif yayi Allah wadai da wannan hari da ya kira na “matsorata.”

XS
SM
MD
LG