Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kai Hari Suka Saci Wasu 'Yan Kasar China a Cikin Kamaru


Map of Waza, Cameroon
Map of Waza, Cameroon

Rahotanni daga Waza mai tazarar kilomita 15 kacal daga bakin iyaka da Jihar Bornon Najeriya na cewa maharan su 200 sun kuma kashe wani sojan Kamaru guda daya.

'Yan Boko Haram sun kai farmaki a kan garin Waza dake Lardin Arewa mai Nisa ta kasar Kamaru, inda suka saci wasu ininiyoyi 10 'yan kasar China, suka kuma kashe sojan Kamaru guda daya.

Wannan harin yazo 'yan sa'o'i kadan kafin a fara taron koli kan kungiyar ta Boko Haram a Paris, babban birnin Faransa, inda shugabannin kasashe biyar, cikinsu har da na Najeriya, suka gana domin shata yadda kasashen yankin zasu iya hada kai wajen yakar kungiyar ta tsageranci.

Rahotanni sun ce 'yan Boko Haram su kimanin 200 sun kai farmaki a kan garin Waza. Garin na Waza yana da tazarar kilomita 15 kawai daga iyaka da Jihar Borno, inda kungiyar take da cibiya.

Wani mazaunin garin Waza, Djibrilla Toukour, ya fadawa VOA cewa maharan sun shiga cikin Waza da tsakar dare a kwambar motoci, inda suka fara bude wuta.

Maharan sun kashe wani sojan Kamaru, a kusa da wani sansani inda injiniyoyi 'yan kasar China masu aikin gina hanya suke zaune, suka dauke motocin injiniyoyin. Toukour yace hukumomi ba su gani ko kuma san inda wadannan 'yan China suke ba, abinda yasa ake zaton sace su aka yi.

Gwamnan Lardin Arewa mai Nisa, Fonka Awah Augustine, yace an girka sojojin Kamaru cikin gaggawa a bakin iyaka domin hana maharan tserewa su koma cikin Najeriya. Yace akwai yiwuwar cewa har yanzu wasu daga cikin maharan su na nan a Kamaru.
XS
SM
MD
LG