Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijiran Najeriya A Kasashen dake Makwaftaka da Kasar Suna Komawa


Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Moh Bindo Umaru Jibrilla da Hajiya Sadiya Umar Faruk Kwamishaniyar hukumar kula da wadanda suka rasa muhallansu
Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Moh Bindo Umaru Jibrilla da Hajiya Sadiya Umar Faruk Kwamishaniyar hukumar kula da wadanda suka rasa muhallansu

Kamar yadda alkalumman hukumomin bada agaji da kuma na kula da yan gudun hijira ke nunawa,kawo yanzu sama da yan gudun hijira yan Najeriya dubu talatin ne suka komo gida daga kasashen Kamaru,Nijar da kuma Chadi,biyo bayan kwanciyar hankalin da aka soma samu a yanzu.

Wannan ma kuwa na zuwa ne yayin da hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA, kema kai wasu kayakin tallafi ga yan Najeriyan dake gudun hijira a Kamaru sakamakon rikicin na Boko Haram,wanda yayi sanadiyar asarar dubban rayuka a Najeriya da wasu kasashen dake makwabtaka da ita.

Hukumar dai ta NEMA, tace yanzu haka yan Najeriyan dake makale a kasashen ketaren na son komowa gida,kasancewar hankula sun soma kwantawa a yankunansu.

Sani Datti dake zama jami’in hulda da jama’a na hukumar NEMA a Najeriya,yace yanzu haka yan Najeriyan na son komowa gida Najeriya.

Kamar dai hukumar NEMA, ita ma hukumar dake da alhakin kula da yan gudun hijira ta Najeriya,wato National Commission For Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons (NCRMI) tuni ta soma zagayawa jihohi ukun nan da rikicin Boko Haram yafi shafa,jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe don ganin halin da yan gudun hijira ke ciki.

A ziyarar kawo kayan tallafi da tawagar hukumar suka kawo jihar Adamawa,babbar kwamishiniyar hukumar Hajiya Sadiya Umar Faruk tace,hukumar a yanzu zata maida hankali ne wajen sake tsugunar da yan gudun hijiran.

Hajiya Sadiya Umar Faruk yayinda take jawabi
Hajiya Sadiya Umar Faruk yayinda take jawabi

Shima da yake jawabi yayin raba kayakin tallafin gwamnan jihar Adamawa,Sen.Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla ya yaba da nasarorin da ake samu yanzu a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.

Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram ya tilastawa gudun hijira,zuwa kasashen waje baya ga wadanda yanzu ke sansanonin da aka tanadar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG