Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARABA: ‘Yan Gudun Hijirar Wukari Sun Koka Ga Shugaban Najeriya - 4'41"


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Akwai ‘yan gudun hijirar da suka warwatsu a jihohi daban-daban makwabtan jihar ta Taraba. Wadanda suka tsre daga muhallansu saboda matsalar hare-haren ta’addanci Boko Haram. Babban kukan ‘yan gudun hijirar shine yadda gwamnatin Taraba ta yi kunnen uwar shegu da su.

Domin a cewarsu, har yau gwamnan jihar bai taba damuwa ya nemesu ya kai ziyarar ganin halin da suke ciki ba, wanda hakan yasa suke kallon kansua matsayin saniyar ware, ko kuma wadanda aka manta da lamarinsu na bakar wahalar da suke ciki.

Wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya tattauna da wasu da dama daga cikinsu, inda suka yi amfani da damar cewa, suna kira ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya daure ya kai musu ziyrar gani da ido tunda Wukarin ba bakuwarsa bace.

Daga nan zai ga yadda aka yi watsi da sub a tare da tallafin da suke ta sa ran samu daga jiharsu ta Taraba ba. Babban kukansu dai shine rashin karatun ‘ya’yansu da noma abin da zasu ci kamar yadda suka saba. To amma a bangaren gwamnatin Taraba sun kare kansu.

Inda babban sakataren hukumar bada tallafin gaggawar jihar Taraba ya bayyana cewa, suna sane da halin da ‘yan gudun hijirar Wukarin ke ciki na rasa muhallansu da gonakinsu da makarantu. Sannan su kara hakuri, suma sun mika kokon bararsu ga gwamantin tarayya na neman agazawa ‘yan gudun hijirar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00

XS
SM
MD
LG