Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwar Jos Sun Bukaci Gwamnati Ta Hanzarta Bude Kasuwar


دنیا بھر سے 20 لاکھ سے زائد افراد حج کی ادائیگی کے لیے سعودی عرب میں ہیں
دنیا بھر سے 20 لاکھ سے زائد افراد حج کی ادائیگی کے لیے سعودی عرب میں ہیں

'yan kasuwar taminus dake garin Jos inda aka kai harin bamabamai makon da ya gabata sun bukaci gwamnati da ta hanzarta sake bude kasuwar

Makon da ya gabata aka kai harin bamabamai akan kasuwar taminus dake tsakiyar garin Jos babban birnin jihar Filato inda mutane fiye d 120 suka rasa rayukansu da asarar miliyoin dukiyoyi.

Sanidiyar harin bamabaman yasa gwamnatin jihar ta rufe kasuwar har sai ta kammala kwashe baraguzan shaguna da gidajen da suka ruguje.

Amma yanzu 'yan kasuwar sun bukaci gwamnati da ta bude kasuwar domin rage matsalar rayuwa da suka shiga ciki. Shugaban 'yan kasuwar Abdulrahaman Jimoh Yusuf yace suna rokon gwamnati da ta gaggauta sake bude kasuwar domin rage matsalar rayuwa dasu da iyalansu ke ciki. Yace gwamnati ta taimaka kada mutuwar ta zama kashi biyu. A taimakawa talakawa tare da bude kasuwar domin su cigaba da kasuwanci. Idan suka cigaba da kasuwanci wannan zai nuna kwanciyar hankali.

A cewar shugaban wasu sai sun fito kasuwa zasu samu abun ciyar da iyalansu. Idan ba'a bude kasuwar ba wasu bata gari ka iya sa komi ya faru.

Shi ma shugaban 'yan kasuwa na jihar Filato Mr. Danjuma Hirse ya kira a kara matakan tsaro a kasuwar. Yace sun yi asarar rayuka fiye da dari biyu da dukiyoyi da suka kai nera biliyan daya sabili da haka suna kiran gwamnati ta inganta tsaro a kasuwar. Ya kira hadin kai da jami'an tsaro domin hana sake aukuwar irin abun da ya faru.

Sakataren kungiya agaji ta Red Cross ya ba gwamnatin jihar shawarar gina kasuwanni a anguwanni domin rage cunkoso a kasuwar taminus.

Kawo yanzu dai gwamnati na cigaba da share kasuwar kuma bata bada sanarwar ranar da zata sake bude kasuwar ba.

Ga rahoton Zainab Babaji.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG