Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

'Yan Kasuwar Nijar Sun Ce Ba Za Su Kara Farashin Kaya Ba


Wani Shagon Saida Kayan Abinci
Wani Shagon Saida Kayan Abinci

Shugabannin ‘yan kasuwa a Jamhuriyar Nijar sun yi ittifakin cewa ba za su kara farashin kayan masarufi ba, yayin da ake shirin tunkarar azumin watan Ramadana

Dama a kowace shekara masu fada a ji su kan yi taron gabanin fara azumin domin daukan alkawarin kauracewa kara farashin kayayyaki domin kada a muzgunawa al’uma.

A irin wannan lokaci akan samu ‘yan kasuwa da ke amfani da watan na azumi wajen kara farashin kayayyakin masarufi domin a lokacin ne magidanta suka fi shiga kasuwanni domin sayen musamman kayan abinci.

To sai dai wasu magidanta a Jamhuriyar ta Nijar, sun nuna shakkunsu dangane da wannan matsaya da ‘yan kasuwar suka dauka domin a cewar su ba dukkanin ‘yan kasuwan ne su ke bin umurnin ba.

Domin jin karin bayanin kan wannan batu, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

XS
SM
MD
LG