Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Kasuwar Nijer Da Na Tunisia Sun Gudanar Da Babban Taro


Samar da sassaucin gudanar da al’amuran kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijer dake sa ran juya harkokin su zuwa kasar Tunisia, kamar yadda kasar ta Tunisia ke fatan a bata dama ta fitar da wasu hajjojin da take bukata daga wajan kasar Nijer.

Wannan ne makasudin hada wannan taro da gwamnatocin kasashen Biyu suka shirya da zummar kara karfafa hulda da cudanya tsakanin ‘yan kasuwa.

M. Sidi Mohammed, shine shugaban hukumar bunkasa kasuwancin jamhuriyar Nijer, ya bayyana cewa wannan dama ce da ‘yan kasuwar zasu hadu da takwarorinsu a maimakon yin tattaki zuwa wata kasa kafin su gamu da wasu ‘yan kasuwar.

Da dama daga cikin ‘yan kasuwar na jamhuriyar Nijer, suka fara nuna gamsuwa da takwarorin nasu bayan wannan ganawa.

Ko baya ga harkokin saye da sayarwa a tsakanin kasashen Biyu, firayin ministan kasar Tunisia, ya bukaci ‘yan kasuwa da hukumomin kasar su duba hanyoyin kafa kamfanoni da masana’antu a janhuriya Nijer, ta yadda za a bude hanyoyin saka hannayen jari ga masu bukata.

A yayin da ake gudanar da wannan babban taron hadin gwiwa, hukumomin kasuwancin kasar Nijer, da takwarorinsu na kasar Tunisia, sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya wadda a karkashinta dukkan kasashen biyu suka dauki alwashin bada kariya ga dukkan dan kasuwar da ya sami matsala daga cikin kashen Biyu.

Daga Janhuriyar Nijer, ga rahoton Sule Mumini Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG