Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fama da Cutar Polio A Najeriya Sun Yi Roko Ga Iyaye


Ana diga ma wani yaro maganin rigakafin cutar Polio a Mogadishu, babban birnin Somaliya.
Ana diga ma wani yaro maganin rigakafin cutar Polio a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Kungiyar masu fama da cutar Polio ta Najeriya ta roki iyaye da su yi wa Allah su kai 'ya'yansu a ba su maganin hana kamuwa da wannan cuta mai janyo nakkasa

Kungiyar Masu fama da cutar polio ta Najeriya ta yi roko da babbar murya ga iyaye kan su kyale a diga ma 'ya'yansu 'yan kasa da shekara biyar maganin hana kamuwa da cutar mai nakkasa jikin duk wanda ta kama.

Shugaban kungiyar na kasa, Misbahu Lawan Didi, yace duk yaron da ya kaucewa karbar maganin a duk zagaye guda na yin rigakafin, yana jefa kansa da sauran yara cikin kasadar kamuwa da kwayar cutar dake haddasa wannan nakkasa.

A lokacin da yake magana a madadin wannan kungiya ta su mai dubban membobi a fadin Najeriya, Malam Misbahu yace a yanzu haka Najeriya ce kadai kasar Afirka da ta rage inda wannan cuta ta Polio ta yi katutu. Yace idan har ba a samu an murkushe wannan cuta a Najeriya ba, to sauran kasashe makwabta ma su na iya harbuwa da ita.

Kungiyar ta kaddamar da wani gagarumin gangami nata na tabbatar da cewa an samu nasarar ayyukan rigakafin wannan cuta a jihohi 15 da suka fi fama da Polio a arewacin Najeriya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG