Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Najeriya Za Su Sayi Motocin Peugeot


Tambarin Peugeot
Tambarin Peugeot

Kan batun sayen motoci da ake fadin cewa itama Majalisar Wakilan Najeriya zatayi, Muryar Amurka ta tattauna da mai magana da yawun Majalisar Wakilan Najeriya, Abdulrazak Namdas, wanda yace basu ce zasu sayi motoci irin na ‘yan Majalisar Dattijai ba, amma zasu sayi motoci kirar Peugeot 508 kuma zasu baiwa kamfanin Najeriya kwangilar wannan motoci ne.

Inda ya kara da cewa basu ne kadai ke sayan motoci ba in aka duba duk ma’aikata a Najeriya, ana sayawa ma’aikata da yawa, da suka hada da Ministoci da Kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi, hakan yasa sayan motocin nasu ba zai zama wani sabon abu ba.

Kan batun cin hanci da rashawa kuwa Abdulrazak yace, sun gano cewa dole sai anyiwa wasu dokoki gyaran fuska idan har anaso a yaki cin hanci, hakan yasa suka duba wasu dokoki kusan 130 domin yi musu gyara, wanda yanzu haka ana aiki kansu.

Idan harma ‘yan Majalisun Wakilai sunyi wasu dokoki dole sai sun aikawa Majalisar Dattawa sun amince kafin ta zama doka. Mai magana da yawun majalisar dai yace idan suka cika shekara guda zasu bayyana nasarar da aka samu.

Saurarin tattaunawa da Abdulrazak Namdas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG