Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Basa Son a Raba Kasar-Indabawa


Wani mutum da iyalinsa bayan sun taso daga sallar idi.
Wani mutum da iyalinsa bayan sun taso daga sallar idi.

Sakataren kwamitin shawarwari kan taron kasa yace basu sami wata shawara na neman a raba kasar ba zuwa yanzu.

Babban sakataren kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin ya duba hanyoyin da za'a bi domin a gudanar da taron kasa Dr. Akilu Sani Indabawa, ya yaba da ganin cewa har zuwa yanzu kwamitin bai karbi wata shawara ko kasida da ta bukaci a raba kan Najeriya ba.

Dr. Indabawa wanda ya bayyana haka ne bayan zaman wuni daya da kwamitin yayi a Jos fadar jihar Flato, yace kwamitin ya karbi rubutattun shawarwari 34, yace ya fito fili kenan cewa 'yan Najeriya basa son ganin kasar ta wargaje.

Cikin wadanda suka gabatar da shawarwari har da Parfessa Jerry Gana, a matsayinsa na shugaban kananan kabilu 14 d a suke cikin jihohin arewa 14. Parfessa Gana ya gayawa wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji cewa, bukatar da ya gabatar sun hada da ganin an gudanar da taron kasa cikin lumana, tabbatar da diyauci da karfafa Najeriya, hanyoyin da za a bi a karfafa tattalin arzikinta sabo da 'yan kasa duka su sami kayan more rayuwa.

Da yake amsa tambayar cewa baya ganin aikin wannan kwamiti d a taron na kasa duka, hakki ne na 'yan majalisa, Parfessa Gana yace hakika kasancewa akwai 'yan majalisa ya taimaka wajen warware wasu matsaloli, amma har yanzu ga matsalolin rashin zaman lafiya.

Shugaban kungiyar da ake kira Jasawa Elders Foundation injiniya Mansur Salihu Nakande, yace abunda ya fi dacewa shine shugaban kasa ya kira taron da zai tantance makomar Najeriya. Yace aganinsa shine abu mafi a'ala, domin duk wani yunkurin sulhu da aka yi ba ya dorewa.

Nakande yace kamin a yi haka, tilas shugaban kasa da 'yan majalisa na tarayya da jihohi da gwamnoni su sauka daga kan iko da suke rike da su, su mika aikinsu ga bangaren shari'a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG