Accessibility links

Yau ‘yan Najeriya suke bukukuwan ranar kodago ta duniya tare da kokawa dangane da rashin kyautatawa ma’aikata.

Wadansu masu kula da lamura sun bayyana takaicin ganin yadda lamura ke kara tabarbarcewa yayinda ake ci gaba da keta hakin ma’aikata. Suka kuma zargi kungiyar kodago ta kasa a matsayin ‘yar amshin shata kasancewa bata yin tsayin daka wajen kwato hakkkin membobinta kamar yadda aka saba.

Sai dai kungiyar Kwadago ta musanta wannan zargi da cewa, tana iyakar kokari wajen kare hakkin membobinta da kuma sauke hakin da ya rataya a kanta iyaka iyawa.
Wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa ya yi nazarin wannan rana ya kuma hada rahoto.

XS
SM
MD
LG