Kungiyoyin agaji suka ce akalla mutane dubu uku ne suke zaune a sansanin.
Anga bakin haure da dama rike da kayayyakinsu suna dakon motoci da zasu kai su a wasu cibiyoyi inda za'a tanatance su.
'Yansanda sun isa sansanin ne da subahi su farkarda mutanen wadanda suke barci a cikin tantuna ko akan katifu, wasu daga cikinsu sun rude kuma suna cikin damuwa domin basu san ind a za'a kai su ba.
Wannan matakin da 'Yan sandan suka dauka yana zuwa ne mako daya baya da shugaban kasar Francois Hollande ya bada umarnin a tarwatsa sansanin dake Kalay.