Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Yi Arangama Da Masu Bore a Angola


Shugaban Angola Eduardo dos Santos
Shugaban Angola Eduardo dos Santos

Wani babban jami’in tsaro a Angola, Kanar Silvano Ndogua, ya zargi gamayyar ‘yan adawa da su ka yi zanga zanga da laifin ta da tarzomar da ta kai ga wasu sojoji su ka harbe wani matashi har lahira a babban birnin kasar a makon da ya gabata, da kuma wasu masu rusau da suka yi sanadin mutuwar wani jariri.

Sai dai jam’iyar adawa ta UNITA, ta yi Allah wadai da zargin tare da kwatanta lamarin a matsayin “karya.”

Zanga zangar wacce aka yi a ranar 6 ga watan Agusta a unguwar Zango da ke Luanda, bore ne ga jam’iyar MPLA, wacce ta jima ta ke mulkin kasar tun daga tun daga lokacin da ta samu ‘yan cin kai a shekarar 1975 daga hanun turawan mulkin mallaka na kasar Portugal.

Ana zargin jam’iyar ta MPLA ta wawure dukiyar kasar yayin da al’umar kasar ke cikin kangin talauci.

Mazauna yankin na Zango sun yi zanga zangar lumana ce kan wani shirin rushe masu gidaje domin fadada ayyukan gwamnati na ci gaba a yankin, wadanda su ka shaida lamarin su ka gayawa kungiyoyin kare hakkin bil’adama.

Su dai hukumomin sun ce mutanen unguwar sun yi gine-gine ne a wani wuri da aka tanada domin gina sabuwar tashar jiragen sama.

XS
SM
MD
LG