Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Dan Kunar Bakin Wake a Damaturu


Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan Yobe
Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan Yobe

Wani dan kunar bakin wake da ya nufi ofishin 'yan sanda da mota cike makil da bamabamai a Damaturu dubunsa ta cika.

Wani dan kunar bakin wake da ya so ya kai hari akan ofishin 'yan sanda dake Damaturu ya fada hannun 'yan sandan kuma yanzu yana hucewa a wurinsu.

Rundunar 'yan sandan jihar Yobe tace ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 19 da ya tuka mota cike da bamabamai da yayi niyar kutsawa cikin harabar 'yan sandan. Kwamishanan 'yan sandan jihar Sanusi Rufai shi ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Muhammed Fawu yadda lamarin ya faru.

Jiya Lahadi da safe da misalin karfe takwas da wasu mintoci wani Abubakar Sadiq Umar dan shekara 19 da haihuwa ya tuko mota akori kura dauke da ciyawa ta dabbobi amma a karkashin ciyawar an shirya bamabamai. Ya yiwo kukan kura yana son ya shiga ofishin 'yan sandan. Da suka tsayar dashi sai ya ki tsayawa su kuma suka harba bindiga lamarin da ya bashi tsoro. Sai ya fita da gudu amma aka kamashi. Suna bincikar motar sai suka ga bamabamai da aka shirya.

A cikin firar da suka yi da yaron ya fadawa 'yan sanda cewa wajen wata uku ake nan da 'yan Boko Haram suka sameshi a Talala cikin jihar Borno suka horas da shi daga bisani kuma suka turoshi ya aiwatar da ta'adancin.

Bangaren 'yan sanda dake kula da bamabamai ya lalata bamabaman da yaron ya tuko cikin mota.

Mazauna garin Damaturu sun ce suna zaman lafiya, babu wata matsala. Kowa yana walwala kodayake an tsaurara matakan tsaro.

Ga rahoton Sa'adatu Muhammed Fawu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG