Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Yi Cirko-Cirko Da Dan Bindiga A Faransa


'Yan sandan su na kokarin lallashin mutumin da ya mika kai, bayan da aka yi musanyar wuta a lokacin da suka yi yunkurin shiga gidansa don kama shi.

‘Yan sandan Faransa su na kokarin lallashin wani mutumin da ake zargi da laifin harbe mutane 7 har lahira, cikinsu harda yara uku kanana na wata makarantar Yahudawa a birnin Toulouse, domin ya mika kansa.

Jami’ai suka ce wannan mutumin mai suna Mohammed Merah, dan shekaru 24 da haihuwa, dan kasar Faransa ne tsatson Aljeriya, wanda yayi ikirarin cewa shi dan al-Qa’ida ne, kuma an taba kama shi aka tsare a kasar Afghanistan.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Claude Guent, yace ‘yan sanda sun kuduri aniyar kama Merah da ransa. ‘Yan sanda biyu sun ji rauni a yunkurin farko da aka yi kafin wayewar gari na far ma gidan da yake ciki a Toulouse, inda aka yi ta musanyar wuta.

Jim kadan a bayan wannan ne ‘yan sanda suka kama wani dan’uwansa.

Guent yace wanda suke zargin ya fusata da matakan sojan da Faransa take dauka a kasashen waje, ya kuma ce ya so ne ya dauki fansar yaran Falasdinawa da aka kashe a Gabas ta Tsakiya. Firayim ministan Falasdinawa, Salam Fayyad, yayi tur da kashe-kashen yana mai fadin cewa lokaci yayi da masu aikata laifi zasu daina amfani da sunan Falasdinawa wajen kafa hujjar danyen aikinsu.

XS
SM
MD
LG