Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kungiyar Shiya Sun Mayar da Martani Kan Cigaba da Tsare Shugabansu da Dasuki


Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky
Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky

Kungiyar yan uwa Musulmi a Najeriya ,lauyoyi da kuma masana sun maida martani game da dalilan da fadar shugaban Najeriya ta bayyana na cigaba da tsare tsohon mashawarcin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da shugaban Kungiyar 'yanuwa Musulmi mabiya mazhabar Shi'a Sheikh Ibrahim Yakubu El- Zakzaky.

Malam Garba Shehu, dake zama hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai a jiya talata ya ce, gwamnati bata da niyar musgunawa El-Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a Abuja to amma kuma yace tana bashi kariya daga barazanar da ka iya tashi sakamakon samun 'yancinsa, a yayin da Kanar Sambo Dasuki ke jiran shari’u da gwamnatin kasar.

Ibrahim Musa wanda shine babban editan jaridar Almizan ya shaidawa Muryar Amurka cewa su basu gamsu da hujjar da gwamnatin ta bada ba,ganin cewa kotu ta yi fatali da wannan batu.

Ko a baya dai ,wasu kotunan Najeriya dama na wajen kasar da suka hada da kotun yankin yammacin Africa, duk sun bada umarnin sakin Kanar Dasuki da ake zargi da almubazzaranci da kudin yaki da ta’addanci kusan Dalar Amurka miliyan dubu biyu da dari daya to amma kawo yanzu ba’a sake shi ba.

Kanar Sambo Dasuki wanda ake zargin yin zarmiya da kudin sayen makamai
Kanar Sambo Dasuki wanda ake zargin yin zarmiya da kudin sayen makamai

To ko me masana sharia ke cewa ne game da wannan batu? Barr. Ibrahim Muhammad Gwary wani lauya ne mai zaman kansa a Najeriya na ganin akwai abun dubawa game da rashin bin umarnin kotu da ake zargin gwamnatin Buhari na yi.

Batun tun ba yau ba ne dai kungiyoyin kare hakkin bani adama na ciki dama wajen Najeriya ke kiran gwamnatin kasar da ta saki jagoran yan uwa Musulmi Shiekh Ibrahim Zakzaky, kamar yadda ta saki Nmandi Kanu jagoran fafutukar neman kafa kasar Biafra.To ko hakan me ke nunawa? Dr Aliyu Tilde wani manazarci ne a Najeriya yace akwai abun dubawa game da batun cigaba da tsare Dasuki da El-Zak Zaky.

Idan dai za’a iya tunawa a tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Disamban shekarar 2015, aka samu arangama a tsakanin sojojin Najeriya da kuma yan kungiyar ta yan uwa Musulmi inda aka samu asarar rayuka a garin Zaria da ke arewacin kasar. Sai dai har yanzu babu alamun sulhu tsakanin gwamnati da kuma yan kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG