Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takara Bakwai Ne Zasu Fafata A Zaben Shugaban Kasar Ghana


Shugaban Ghana John Mahama Dramani
Shugaban Ghana John Mahama Dramani

Hukumar zaben Ghana ta tabbatar da yan takara shugaban kasa bakwai a babban zaben kasar na ranar bakwai ga watan Desimba.

'Yan takara da suka yi nasarar shiga zaben kuwa da suka hada da masu jagorantar jami’iyyu shida da dan independa guda, sun kwana hukumar zaben jiya Laraba a birnin Accra wurin shirya yanda hotunansu zasu bayyana a kan takardun zabe.

Yan takarar zasu bayyana ne a kan takardan zaben ne kamar, Jami’iya CPP ta Kwame Nkrumah itace farko, sai NDP ta uwargidan Rawlings ta biyu, jami’iyar NDC mai mulki itace ta uku, sa’annan jam’iyar PPP tana ta hudu, babbar jami’iyar dawa ta NPP itace ta biyar, sa’annan PNC mai kwakwa ta shida sai kuma dan independa Jacob Osei Yeboah na karshe.

Da farko hukumar zaben ta dakatar da wasu yan takara sakamakon gazawarsu wurin cike takardun shiga takara, amma jam’iyyun PPP da NDP da sauransu sun kalubalanci wannan abu a kotu. A wani hukunci da kotu ta zantar na cewar hukumar zaben ta ba ‘yan takaran lokaci su gyara kura kuran takardun nasu.

XS
SM
MD
LG