Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Amurka Sun Karfafa Neman Zabe Mataimakansu Kuma Zasu Yi Muhawararsa Daya Tak


Dan takara Trump da 'yar takara Clinton
Dan takara Trump da 'yar takara Clinton

Yau Talata dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump zai gudanar da yakin neman zabe a jihar Arizona da ke yammacin Amurka, yayinda ita kuma Hillary Clinton ta tattara magoya bayanta a jihar Pennsylvania, amma hankali duka ya karkata ne kan jihar Virginia inda mataimakan ‘yan takarar zasu gudanar da muhawara tsakaninsu sau daya tilo kafin ranar zabe wanda za a yi ranar 8 ga watan Nuwambar wannan shekarar.

Karawar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Repblican Mike Pence da Tim Kiane na Democrat yana zuwa ne kwanaki kacal, kamin Donald Trump da Hillary Clinton su kara a karo na biyu.

Jiya Litinin ‘yan takarar guda biyu sun ci gaba da sukar juna, inda Ms. Clinton ta caccaki Trump akan batun haraji shi kuma Trump ya caccake ta akan batun yin amfani da adireshin email wanda ba na gwamnati ba yayinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka.

A wani gangami da tayi a jihar Ohio wacce take da matukar tasiri a zaben nan, Clinton ta fadi cewa Trump ya fito ne daga “irin tsarin nan da baya mutunta mai karamin karfi, kuma zai kara karfafa shi muddin ya zama shugaban kasa.”

Ms. Clinton ta danganta sabon zarginta akan Trump biyo bayan rahoton jaridar NEW York Times wanda ya nuna harajin dan takarar na jam’iyyar Republican na shekarar aluf dari tara da cisi’in da biyar inda ya bayyana cewa yayi hasarar dala miliyan 916 daga sana’arsa ta caca da kuma wasu sana’o’in. irin wannan adadin ka iya sa attajirin mai sana’ar saida gidaje ya kaucewa biyan haraji har na tsawon shekaru 18 a hukumance.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG