Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Faransa Sun Gwabza Muhawara


Yan takarar zaben shugaban kasar Faransa Marine Le Pen da Emmanuel Macron sun gwabza a wata zazzafar mahawara ta sa’o’i biyu a talabijin a jiya Laraba, ana saura yan kwanaki kafin gudanar da zaben zagaye na biyu.

Le Pen ta bayyana abokin karawarta da cewa dan jari hujja ne mara tausayi mai rauni a kan ta’addanci, a yayinda Macron kuma ya kirata makaryaciya mai tsattsauran ra’ayi kuma abar tsoro.

A cikin jawabinta na sharan fage, Le Pen ta kira tsohon mininstan tattalin arziki Macron a matsayin dan takarar da bai san inda duniya ta nufa ba. Shiko Macron kira Le Pen wacce ta taba tilastawa mahaifinta mai tsaurin ra’ayin gurguzu ficewa daga jami’iyarsu ta National Front a matsayin yar gadon jam’iyar gurguzun Faransa.

Tsananin rashin aikin yin a cikin abubuwa da mahawara ta maida hankali akai. Macron ya yi kira da gwamnati ta sassautawa kananan da matsakaitan kasuwanci, a yayinda Le Pen ta yi alkawarin dora haraji a kan kampanoni da zasu dauko ma’aikata daga waje.

A kan batun ta’addacin da ya yi sanadiyar mutuwar Faransawa 240 tsakanin shekaru biyu, Le Pen ta yi kira da a rufe masallatai da ake zaton suna yada akidar ta’ddanci kuma a fadada gidajen yari kana a karfafa matakan tsaro a iyakokin Faransa. Shi kuma Macron yace yakamata a kara sa ido a kan duniyar gizo, a samar da jami’an yan sanda masu yawa kuma a inganta musayar bayanan sirri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG