Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye Sun Kwace Wasu Muhimman Tashoshin Ruwa a Libya


Dakarun dake karkasahin dan tawayen nan na kasar Libya, Janar Khalifa Haftar, sun bayyana cewa sun samu nasarar kwace wasu muhimman tasoshin jiragen ruwan jigilar mai biyu dake gabashin kasar ta Libya.

Bayan a farkon wanna watan ne duka sassan biyu suka fada hannun kungiyar nan ta masu tsattsauran ra’ayin addini.

Libya dai ta fada cikin rudu da damuwa ne wanda ya haifar da rarrabuwar kawuna ta fannin mulkin kasar da kuma rundunar sojoji daban-daban, tun a cikin shekarar 2011 bayan da aka kifar tsohuwar gwamnatin marigayi Mu’ammar Ghadaffi, shi kuma aka kashe shi.

Tun daga wannan lokacin ne aka samu kungiyoyi biyu kowacce da sojojinta na sa kai, kowacce na kokarin ganin ta samu ikon mallakar kasar da ke da arzikin man fetur.

Mai Magana da yawun rundunar, Haftar ya fada jiya talata cewa tasoshin jiragen ruwan dakon mai ta Ras Lanuf da na Al-sidra sun kwace su daga hannun ‘yan jihadin nan da ake kira dakarun tsaron Benghazi baya an kai musu hari ta sama da kasa da kuma ruwa.

Haftar shi da sojojin sa na mara wa sojojin Libyan da ake kira Sojojin Kishin Kasar Libiya (Libyan National Army) da ke tafiyar da mulkin kasar a can birnin Tabruk, sune wadanda suka ki mara wa sojojin da keda goyon bayan MDD wadda aka samar na hadin ka kasa a birnin Tripoli.

Wannan kiki-kakar ta Libya ta jefa kasar dake da mutane sama da miliyan 6 cikin damuwar rashin gwamnati tsayayya na kusan shekaru 6 yanzu.

Jamaa da dama ciki harda maaikatan diflomasiyya sun bayyana kasar ta Libya daya daga cikin kasashen duniya data fada cikin rudu tun lokacin mutuwar shugabanta Mu’ammar Ghadaffi.

Haftar tsohon na hannun damar marigayi shugaba Ghadaffi ya karbe ikon kusan duka albarkatun man kasar, kuma yana bari kudin shigan da ake samu daga wanasn mai yana kaiwa ga babban bankin kasar amma da goyon bayan Rasha wadda tace tilas duk abinda za ayi na gwamnatin hadin kan kasa akasa dashi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG