Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tsagerar Somalia sun kai hari ofishin 'yan sanda


Harin bom a garin Beletweyne na kasar Somalia
Harin bom a garin Beletweyne na kasar Somalia

Tsagerun Matasan Somalia sun kaiwa ofishin 'yansandan Somalia hari.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da rahoton cewar tsagerun 'yan jihadin Islama sun tada boma-boman mota jiya talata a kofar shiga Tashar Beletweyne dake Somalia, kuma wasu gungun matasa hudu dauke da makamai sun kutsa cikin ginin.

Jami'ai sun bayyana cewar 'yan tsagerar sun kaiwa mutane masu yawa hare-haren ta'addanci, cikinsu harda jami'an 'yan sanda, an kuma kashe farar hula masu yawa. Su dai 'yan kungiyar al-Shabab sun yi ikrarin cewar sune ke kai irin wadannan hare-haren a kan farar hula, sun kuma kashe mutane masu yawa 'yan Somalia da 'yan kasar Djibouti.

Kasar Djibouti dai, na daya daga cikin kasashen dake bada agajin sojin dake tallafawa rundunar sojin kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka dake Somalia. Idan an tuna, a watan da ya gabata ne kungiyar Al-shabab tayi ikrarin cewar ita keda alhakin kai harin bom a gidan cin abinchi Beletweyne inda har aka kashe akalla mutane 15.
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG