Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Haramta Kalamun Batanci


'Yansanda suna sintiri.
'Yansanda suna sintiri.

Yayin da ya rage kasa da makonni shida a gudanar da zabukan Najeriya Kwamishanan 'yansandan jihar Borno yace ba zai lamunta wa duk wani dan siyasa da ya nemi tada zaune tsaye yayin da yake fafitikar neman kuri'u a jihar.

Kwamishanan Mr.Clement Aduda ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wani taro da yayi da 'yan siyasa a hedkwatar 'yansandan a Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Kwamisahanan yace irin rigingimu na hare-hare da rashin zaman lafiya da suka addabi al'ummar jihar sun isa. Sabili da haka bai kamata wani dan siyasa yace zai tada hankali ko kuma yayi anfani da kalmomin batanci akan 'yan siyasa 'yanuwansa ba.

Kwamishanan yace ashirye yake ya saka kafar wando daya da duk wani dan siyasa da yayi anfani da kalamun batanci lokacin yakin neman zabe. Ya zama wajibi kwamishanan yayi kashhedin domin birnin Maiduguri ya cika ya batse da kwararowar 'yan gudun hijira wadanda 'yan Boko Haram suka rabasu da muhallansu suka kuma mamaye kananan hukumominsu. Hatta wasu barikokin sojoji basu tsira ba.

Lamarin dake faruwa ya sa shakka a zukatan jama'a ko hukumar zabe zata iya gudanar da zaben kamar yadda ta kuduri yi.

'Yansiyasa daga jam'iyyu daban daban sun fadi albarkacin bakinsu akan yiwuwar zaben. Aminu Abubakar Gwandu na jam'iyyar PDM yace shirye-shiryensu sun ta'allaka ne akan hukumar zabe ta INEC. Yace har yanzu INEC bata fara raba katin zabe na dindindin ba a jihar Borno. Tambaya nan ita ce da menene za'a yi zabe? Sabili da haka suna shakkar ko za'a yi zaben.

Duk 'yansiyasar jihar sun goyi bayan a yi zabe koda ma za'a yi ne a sansanin 'yan gudun hijira.

Ga rahoton rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG