Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Faransa Sun Tantance Mutum Na Biyu da Ya Kai Hari Kan Wani Coci


Masu juyayi sun sa furanni a cocin da aka kai hari
Masu juyayi sun sa furanni a cocin da aka kai hari

‘Yan sanda a kasar Faransa sun tantance mutum na biyu da ke da hannu a mummunan harin da aka kai a wata cochi cikin farkon makon nan wanda yayi sanadiyyar mutuwar wani limamin cocin.

Abdel Malik Petitjean, dan shekaru 19 da haihuwa, an haifeshi ne a gabashin Faransa kuma hukumomin kasar sun gano shi ne a lokacin da yayi kokarin zuwa Siriyya. ‘Yan sandan sun iya tantance shi bayan da aka gwada kwayoyin hallitar mahaifiyarsa da ake kira DNA.

Petitjean da kuma Abdel Kermiche, shima dan shekara 19 da haihuwa, sun afkawa cocin saint Etienne-du-Rouvray a arewacin Faransa a lokacin da ake sujadar safe, inda suka yanka wani limamin coci dan shekara tamanin da shidda da haihuwa suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 5. Daga baya ‘yan sanda suka harbe maharan biyu, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwar da shi kuma yana cikin mawuyacin hali.

Dama Kermiche na jiran shari’a akan laifukan da suka shafi ta’addanci, kuma ya sanya wani awarwaron lantarki a lokacin suka gudanar da farmakin.

XS
SM
MD
LG