Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara miliyan biyu da dubu dari shidda ke mutuwa a duk shekara


Wani yaro zaune yana kallon dubban mutanen da suka rasa muhallinsu.
Wani yaro zaune yana kallon dubban mutanen da suka rasa muhallinsu.

Wani sabon bincike ya gano . a duk shekara yara kusan miliyan uku ke suka mutuwa, a saboda rashin kayayyakin abincin gina jiki.

Wani sabon binciken ya gano cewa yara miliyan biyu da dubu dari shidda suna mutuwa a duk shekara a saboda rashin kayayyakin abincin gina jiki,.

Kungiyar ceton yara da ake cewa Save the Children da turanci ce ta rubuta wannan rahoto. Kungiyar Save the Children tace duk da yunkurin da ake yi na kawo karshen yunwa a duniya, rashin kayayyakin abincin gina jiki na ci gaba da zama matsalar da aka yi watsi da ita ko kuma ake yiwa daukar sakainar kashi, wadda ta adabi rubu'i daya na yara a duk fadin duniya.

Wannan bincike da aka gudanar a watanin Disamba da Janairu, yace cikin kowane sa'a guda yara dari uku ke mutuwa a saboda rashin kayayyakin abincin gina jiki.

Kungiyar Save the Children ta hauhauwar farashin kayayyakin abinci ta tilastawa yara a kasashen duniya da dama barin makaranta domin su taimaki iyalinsu wajen samu kudi.

Galibi kuma wasu iyalan ba zasu iya sayen kayayyakin abincin gina jiki ba. A saboda haka kungiyar Save the Children take rokon Prime Ministan Ingila David Cameron da ya yiwa Allah ya gudanar da taron koli akan matsalar yunwa a gefen wasanin Olympics da za'a yi a bana a birnin London.

Kungiyar Save the Children tace ana iya ceton kashi casa'in daga ciki dari na yaran da suka fi tagaiyara daga rashin kayayyakin abincin gina jiki da dala biliyan goma a duk shekara.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG