Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar da Majalisar Dinkin Duniya Ta Kebe ta Tunawa da Sufuri Kan Teku


Jiragen ruwa dake dakon kaya daga kasa zuwa kasa
Jiragen ruwa dake dakon kaya daga kasa zuwa kasa

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta kebe kowace ranar 29 ga watan Satumbar kowace shekara, a matsayin ranar tunawa da sufuri da jiragen ruwa kan tekun duniya, hanyar sufurin da tafi dadewa a duniya.

Taken bikin tunawa da sufuri a kan tekuna duniya na wannan shekarar shi ne "Sufurin Jiragen Ruwa Abun Dogaro Ga Al'ummar Duniya".

A sakon da ya aikawa duniya babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya nuna yadda kasashe da al'ummomi daban daban suka dogara ga safaran kayan da ake shigowa dasu kasashensu ta jiragen ruwa amma kuma ba duka al'ummomin suka san da hakan ba.

A cewar Ban Ki-moon akasarin kayayyakin abinci da na masana'antu da kuma magunguna da yawansu ya kai kusan kashi 70 cikin 100 ana shigo dasu ne ta sufurin jiragen ruwa a tashoshi daban daban na kasashen duniya.

A Najeriya akwai tashoshin jiragen ruwa guda shida amma wasu matakan da gwamnatocin baya suka dauka ya sa yawancin 'yan kasuwar kasar kauracewa tashoshin suna yin anfani da na mawafcin kasashe irinsu Kwatano a jamhuriyar Benin ko Lome ta kasar Togo har ma da Tema a kasar Ghana.

Cikin wadannan matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka sun hada da kara haraji kan motoci daga kashi 20 cikin dari zuwa kashi 70 cikin dari lamarin da ya haddasa tsadar motocin da ake shigowa dasu daga kasashen ketare.

Akwai kuma matsalar 'yan fashi akan teku da kasar take fuskanta da kuma garkuwa da ma'aikatan jiragen ruwa.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG