Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya'u Daukacin Al'umar Musulmin Duniya Ke Bikin Sabuwar Shekara


Koda yake lissafi ya kan sha ban ban a tsakanin al’umar Musulumin duniya

Kamar dai kowace shekara walau da bi ladiya ko kuma na Musulunci jama’a da daman a gudanar da bukukuwa tare da aduo’I na samu falalar wannan shekara.

Koda yake lissafi ya kan sha ban ban a tsakanin al’umar Musulumin duniya dan tabbatar da ranar daya ga watan Al Muharram, baki yazo daya tsakanin al’uman Musulmin duniya masamman Malamai na ganin cewa an gimama watan na al Muharram, bisa la’akari da tasirin sa a tsakanin al’umar Musulmi a duniya.

A yayi da ake bayyana mahimmanci wannan rana a tarihin Islama, a Najeriya, inda ake da yawan al’umar Musulmai kuma ake gudanar da harkokin Gwamnati da na ya’u da kullum tare da watan bi ladiya yasa akasarin alumar Musulmai basu sanin shiga ko fitar sabon watan na Islama, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Saida kuma domin nuna mahimmacin da wannan rana ke dashi a tsakanin al’umar Musulmai wasu jihohin arewacin Najeriya, dake da rinjayen al’umar Musulmai na bada hutun aiki ko gudanar da wasu bukukuwa a Masallatai da cibiyoyi da makarantu domin girmama wannan wata na sabon shekaran Musulunci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG