Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Kiristoci Ke Bikin Easter A Fadin Duniya


Easter lokaci ne na nuna kauna da kuma ceto ga mabiya addinin kirista a duk fadin duniya cikin salama.

Dubban mabiya Addinin Kirista ne suka daure wa bincike da kuma shingayen tsaro da aka kafa a Dandalin Sain’t Peters Square, wanda aka cika shi da Furanni domin bikin Easter da kuma addu’a ta Fafaroma Francis ta shekara shekara, Bayanin na Easter mai taken “Urbi et Orbi” wato “Zuwa ga birni; zuwa kuma ga duniya baki daya.”

Kiristoci a fadin duniya na bikin Easter a yau Lahadi – ranar da suka yi imanin cewa Yesu Almasihu ya tashi daga mutuwa. Wannan ita ce rana mafi tsarki a Kalandar Kiristoci.

Bikin Mabiya Addinin Kirista na Easter bikine da yake jujjuyawa, yana zuwa ne akan ranaku daban daban a kowacce shekara. Cocin mabiya addinin Kirista na kasashen yamma na bikin Easter ne a duk ranar Lahadin da ta biyo bayan Cikar Wata bayan rana ta daidaita da tsakiyar duniya. Wanda ake kira a turance (Vernal Equinox).

Amma wannna shekarar ranar da ‘yan darikar Roman Katolika da kuma na Protestant suke bikin Easter ya zo daidai da dana Cocin dake bin dadaddiyar akidar Kiristanci ta “Orthodox.” Akasari Bikin Easter na zuwa ne sati guda tsakanin juna , saboda Cocin Kiristoci ta kasashen Yamma na amfani ne da Kalandar Girigori a yayin da Mabiya addinin Kiristanci na Gabashin duniya ke amfani da Tsohuwar kalandar Julian.

Easter dai ita ta kawo karshen sati mai daraja , wanda yake sati ne kafin mutuwar Yesu Almasihu wacce ta hada da Ranar Alhamis wato ranar da Yesu Almasihu yaci abinci na karshe da mabiyansa . Satin mai daraja ya kuma hada da Ranar Juma’a wato ranar da aka gicciye Yesu Almasihu..

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG