Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Kwamitin ECOWAS A Karkashin Jagoranci Shugaba Buhari Zai Isa Gambia


Kwamitin ECOWAS a karkashin jagorancin Shugaba Buhari a Gambia
Kwamitin ECOWAS a karkashin jagorancin Shugaba Buhari a Gambia

A yau Jumu’a ne shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari zai jagoranci wata tawaggar Kungiyar Bunkasa Tattalin Arziki Ta Kasashen Afrika Ta Yamma ta ECOWAS zuwa birnin Banjul na kasar Gambia don ganawa da shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh da kuma shugaba mai jiran gado, Adama Barrow, a cewar kakakin fadar shugaban na Nigeria, Femi Adesina.

Tawaggar ta ECOWAS ta kuma kunshi shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, wacce itace ma shugabar ECOWAS din, da shugaba Earnest Bai Koroma na Saliyo da kuma tsohon shugaban Ghana, John Dramani Mahama.

Wannan balaguron nasu zuwa Banjul ci gaba ne da kokarin da suke na warware rikicin siyasar kasar da ya biyo bayan zaben da aka yi a cikin watan Disamba wanda kuma shi Adama Barrow ya lashe, kuma yanzu haka yake ci gaba kimtsawa don daukan rantsuwar kama aiki a ran 19 ga watan nan na Janairu duk kuwa da kalaman da shi shugaba mai barin gado Yahya Jammeh yayi kwanan nan na cewa shi zai ci gaba da zamansa kan kujerar har sai ranarda Kotun Koli ta kasar tashi ta yanke hukunci akan karar da ya shigar, yana kalubalantar zaben.

Sai dai abinda ba tabbas a kansa shine ko idan shugabannin kasashen na Afrika zasuyi nasarar cusawa shi Jammeh ra’ayin ya hakura ya sauka tun kafin ranar rantsarda Adama Barrow ta zo.

Yayinda wannan ke faruwa ne kuma Majalisar Dokokin Nigeria ta jefa kuri’ar amincewa da cewa a yi wa shi shugaba Jammeh tayin yazo a bashi mafakar siyasa a Nigeria don a karfafa mishi gwiwar sauka cikin lumana.

XS
SM
MD
LG