Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba Za a Cigaba Da Zaman Tantance Neil Gorsuch


Neil Gorsuch Ya Ce Babu Wanda Ya Hura Mai Wuta Akan Yadda Zai Yi Aikinsa idan an tabbatar da shi a matsayin alkalin kotun kolin Amurka.

Wani alkalin Amurka mai suna Neil Gorsuch da shugaba Trump ya zaba a matsayin wanda zai cike daya daga cikin guraban alkalan Kotun kolin Amurka zai sake bayyana gaban wani kwamitin majalissar dattijan Amurka yau Laraba don amsa tambayoyi kafin a kada kuri’a akan ya cancanta ko akasin haka, daga nan a turawa sauran ‘yan majalissar sakamakon.

Gorsuch ya fadawa ‘yan kwamitin shari’ar na ‘yan majalissar a lokacin da ya bayyana a gabansu jiya Talata cewa babu wani jami’in gwamnatin shugaba Trump da ya taba hura mai wuta akan ya dauki alkawarin yadda zai jefa kuri’a akan batutuwa masu zafi da za a iya kawo wa kotun nan gaba.

‘Yan jam’iyyar Democrat sunyi wa alkalin tambayoyi da dama akan alkawuran da shugaba Trump yayi lokacin yakin neman zabensa da suka janyo cece-ku-ce, ciki har da batun maido da tsarin azabtarda wadanda ake zaton ‘yan ta’adda ne, da hana musulmai shiga murka, da zaben alkalan da zasu sauya hakkin mata na zubar da ciki wanda kotun kolin Amurka ta yanke a shekarar 1973 a lokacin shari’ar Roe da Wade.

Haka kuma sanatoci daga ‘jam’iyyun biyu sun yi mai tambayoyi sosai akan tsarin azabtarda ‘yan ta’adda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG