Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Babbar Ranar Zaben Super Tuesday A Amurka


Jihohin da za ayi zaben Super Tuesday a Amurka.
Jihohin da za ayi zaben Super Tuesday a Amurka.

Yau Talata ne ake zaben Gandu a Amurka, wanda ake kira Super Tuesday a turance, inda za a gudanar da zaben jihohi 12 da ya kasance ranar zabe mafi girma cikin wata guda.

Ma’aikaciyar Muryar Amurka Jummai Ali, ta zanta da Shehu Yusuf Kura, tsohon shugaban gidan rediyon Nagarta Kaduna.

Zaben Super Tuesday dai ya samo asali ne a shekara ta 1980 alokacin da jam’iyyar Democrat ta shirya yadda za ayi zabe a jihohin kudancin Amurka, domin wannan yankin ne jam’iyyar ke da karfi sosai kasancewar akwai bakaken fata masu yawa.

Jam’iyyar Democrat dai ta yanke shawara fitowa da wannan tsari na Super Tuesday, domin samun ingatatcen zabe wajen fitar da dan takara yadda shugabannin jam’iyya zasu daura tasiri kan zaben. Haka yasa suka daura hancin jihohi uku da farko, daga nan aka kara suka zama 9, yau kuma gashi an sami har jihohi 13 zasuyi wannan zabe.

Ganin galabar da jam’iyyar Democrat tayi a wannan tsari na zaben fidda dan takara, haka yasa itama takwararta jam’iyyar Republican ta bullo da nata Super Tuesday a shekara ta 1984, ta kuma ce ita zata rikayi a Kudancin Amurka.

Wanann rana ta Super Tuesday na da matukar muhimmanci ga duk yan takarar da suke neman a tsayar dasu takarar neman shugabancin kasar Amurka, kasancewar duk wani dan takara da yake so yayi tasiri a zaben shugaban kasa idan bai taka muhimmiyar rawa a wannan rana ba to kamar za a iya cewa ya hakura kenan.

Saurari Hira da Shehu Yusuf Kura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:15:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG