Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shekaru 48 ke Nan da a ka yi Juyin Mulkin Farko a Najeriya


Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa Firayim Ministan Najeriya Na Farko
Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa Firayim Ministan Najeriya Na Farko

Idan an waiwaya baya an tuna da jiya yau shekaru arba'in da takwas ke nan da a ka yi juyin milkin farko a Najeriya da ya rutsa da Firayim Minista Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da wasu manyan mutane.

A kwana a tashi yau shekaru arba'in da takwas ke nan da a ka yi juyin mulkin farko da ya rutsa da rayukan Sir Abubakar Tafawa da na Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto kuma firimiyan arewa.

A wannan rana ya kamata a waiwaya baya a ga ko dalilin da ya sa sojojin lokacin suka kashe wadannan shugabannin basu yanzu. Shin wai tun lokacin ta sake zani kuwa?

Ranar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga mulkin mallakar Ingila Firayim Ministan lokacin Sir Abubakar Tafawa Balewa ya ce mu 'yan Najeriya ba zamu tilasta kanmu ga kowace kasa ba komi kankantanta. Ya ce za mu yi muamala da kowace kasa a matsayin daya da mu domin ta haka ne kawai za'a samu zaman lafiya da cudanya mai ma'ana a nahiyarmu ta Afirka. To sai gashi yau shekaru arba'in da takwas ke nan da Sir Abubakar Tafawa Balewa ya rasu sanadiyar juyin mulkin da sojoji suka yi. Ranar 15 ga watan Janairu shekarar 1966 ya rasa ransa.

Ban da firayim ministan akwai shugabanni goma sha daya da wannan juyin mulkin ya rutsa da su. Cikinsu har da Sir Ladoke Akintola firimiyan yammacin kasar da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto kuma firimiyan arewacin kasar. A lokacin juyin milkin ne Janaral Agui Ironsi ya karbi ragamar milkin kasar.

Tun daga juyin milkin ne kasar ta shiga da famar juyin mulki daya bayan daya. Kuma a duk lokacin da a ka yi juyin milkin hujjojin da sojojin ke bayarwa basu sauya kamanni ba. Daya daga cikin hujjojinsu shi ne cin hanci da rashawa ko nuna kabilanci ko nuna banbancin siyasa wanda rashin kishin kasa shi ne umalubaisan duk wadannan.

Amma tambaya ita ce daga wannan lokacin da a ka kashe su Sir Abubakar Tafawa Balewa da wasu shugabannin kawo yanzu a na iya cewa an shawo kan matsalolin da sojoji ke cewa su ne dalilinsu na yin juyin mulki? Misali cin hanci da rashawa Aliyu Shettima tsohon shugaban jam'iyyar PRP na jihar Kano ya ce bayan mulkin NPN da GNPP kasar ta kauce hanya. Ya ce yanzu an dauki maganar kishin kasa an ajiyeta gefe daya. Ba kishin kasa a keyi ba. Lokacin su Abubakar Tafawa Balewa babu cuta ba cutarwa. Amma yanzu akwai dubunsu da suke faruwa. Idan aka dauki batun kishin kasa wanene yake kishin kasa yanzu? Ba'a taba nuna banbanci ko na shiya ko na addini kamar yadda a keyi yanzu ba.

Ali Sani malamin kimiya a Kano ya ce babu mafita ga Najeriya sai an dawo mun sake tsarin tunaninmu tun daga kasa har zuwa sama. Ya ce idan ba Allah ba yadda mutane ke jidar dukiyarta Najeriya da tuni ta ruguje.

Amma Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitam Sule cewa ya yi inda duk a ka wurgar da adalci to da wuya lamarin kasar ya dawo daidai. Ya ce a jamhuriya ta farko inda duk dan Najeriya ya je a na girmamashi a na bashi daraja kuma duk inda ya je yana daga kansa. Lokacin dan Najeriya nada mutunci. Amma yau an tsanemu an tsangwamemu. Mun zama ungulu dalili kwa abun da mazan jiya suka bari mun yar. Mutuncin babu. Kamanta gaskiya din babu. Adalcin babu. Son juna babu.Son kasar babu sai abun da ba za'a rasa ba. Duk wadannan suka sa kasar ta tabarbare ya ce domin daga na gaba a ke ganin zurfin ruwa.

Idan aka dubi hujjojin da sojoji suka bayar na yin juyin mulki sai a ga wadannan shugabannin da yanzu basu da rai amma sun fi mutunci a idanun 'yan Najeriya fiye da wadanda suka hambaresu da na yanzu domin da yawansu sun bar duniya ko allura basu bari ba kuma babu kari a kan abun da ya kamata shi ne halaliyarsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG