Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaba Trump Yayi Jawabi A Babban Taron Masu Ra'ayin Rikau


Shugaba Donald Trump yayinda yake jawabi a wurin taron na masu ra'ayin rikau ko CPAC
Shugaba Donald Trump yayinda yake jawabi a wurin taron na masu ra'ayin rikau ko CPAC

Yayinda yake jawabi a babban taron masu ra'ayin rikau shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada sukar da yake yiwa wasu kafofin labarun kasar

A jawabin nasa shugaba Trump yace bai kamata a bar dan jarida ya dinga anfani da majiyar da ba'a tantance ba ko aka sani.

Dubun dubatan magoya bayansa da suka kasance a babban taron na shekara shekara suka ji yana sukar 'yan jarida da yin anfani da kafofin labaran da ba'a sani ba.. Yana cewa yawancinsu suna kago labaran ne kawai domin cimma nasu muradun ko na iyayen gidansu da zummar nuna wa duniya shi mutumin banza ne.

Yace "Na ki jinin wadanda suke kago labarai ba tare da bada tushen labaran ba. Bai kamata a bari su yi anfani da labaran ba saidai idan zasu ambaci sunayen wadanda suka basu labaran" inji Shugaba Trump. Yace babu wasu kafofi kuma.

'Yan jarida sukan sakaya kafofin labarunsu idan abun da suka bada rahoto a kai na amana ne da kuma yana bukatar sirri domin kada wasu da watakila abun ya shafa su nemi fansa ta wata hanya da bata dace ba.

Shugaba Trump ya ambaci, musamman, sunan jaridar Washington Post wadda ta buga wani rahoto wannan watan inda tace tara cikin jami'an leken asiri na yanzu da na da sun fada cewa mai ba shugaban shawara akan harkokin tsaro Michael Flynn ya kara gishiri kan tattaunawar da ta gudana da Jakadan Rasha dangane da batun kakabawa kasar takunkumi.

Shugaba Trump yace mutane taran da aka ambata jaridar ta kirkirosu ne kawai a cikin rahotonta.

"Suna kirkiro nasu kafofin na karya. Basu da gaskiya matuka", inji Shugaba Trump.

Shugaban yace babu wanda ya fi sh son kwaskwarimar farko da aka yiwa kundun tsarin mulkin kasar amma yace 'yan jarida na fakewa dashi su tafka karya a kansa.

Shugaban ya cigaba da cewa yawancin jaridun manya manyan kamfanoni suka mallakesu kuma suna da nasu muradun da ba naku ba ne, inji Trump. Yace ba mutanen kasar suke wakilta ba, ba kuma zasu taba wakiltar mutane ba saboda haka zamu yi wani abu akai, injishi.

Bayan ya gama sukar 'yan jarida shugaba Trump ya bayyana manufofinsa wa kungiyar ra'ayin rikau din wadda yace ita ce ta dace da akidar zama kasa daya kuma zata sa 'ya'yanta gaba a duk harkokinta, wato zata ba 'yan kasa fifiko..

Shugaba Trump ya tabo batun gina takanga tsakanin Amurka da Mexico da kawar da bakin haure muggan mutane dake sayar ko sarafa kwayoyin dake sa maye a kasar. Masu kisan kai , da masu fashi da masu sata da suka fito daga wasu kasashen duka yayi alkawarin fitar dasu daga kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG