Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ta Ke Ranar Yaki Da Polio Ta Duniya


Yawan wadanda ke kamuwa da cutar Polio a Najeriya ya ragu da kasha 50 cikin 100 a bana, amma har yanzu da sauran aiki.

A yayin da duniya take karrama Ranar Yaki da Cutar Shan Inna, ko Polio, har yanzu Najeriya ta kasance cikin kasashe kalilan da suka rage a duniya inda ake samun wannan cuta.

Gwamnati da hukumomin kiwon lafiya na duniya da ma kungiyoyin agaji, sun hada kais u na aiki ba dare ba rana domin yin rigakafin kamuwa da wannan cuta mai nakkasa yara, har ma tana kasha wasu. Amma har yanzu, ba a iya samun kaiwa ga sassan arewacin kasar inda wannan cuta ta fi kanta.

Sai dai kuma duk da haka, Najeriya ta samu tazara sosai a yakin da take yi da cutar ta Polio, wadda aka kawar da ita baki daya daga kasashen yammacin duniya cikin shekatun 1990 a saboda gangamin rigakafin da aka yi ta yi.

A bana, yara 49 ne aka samu sun kamu da cutar ta Polio a Najeriya, watau rabin yaran da suka kamu da ita daidai wannan lokaci a cikin shekarar da ta shige ta 2012.

Babbar jami’ai mai kula da shirin PolioPlus na yaki da cutar Polio a Kungiyar Rotary International a Najeriya, Kemi Lawanson, ta ce kamuwa da cutar babbar ill ace ga yaro da iyayensa domin kuwa idan ta riga ta nakkasa yaro, babu yadda aka iya, zai ci gaba da zama da nakasa har iya tsawon rayuwarsa.

Gwamnatin Najeriya da kungiyoyin agaji sun a kokarin yin rigakafi ga yaran da zasu iya, amma Ms Lawanson ta ce aikin yana da wuya a saboda dari-darin da wasu iyaye keyi da maganin, da kuma harkokin tsaron da suka hana ma’aikatan kiwon lafiya shiga wasu sassan arewa maso gabashin Najeriya.

A bara, babu inda aka samu bullar cutar Polio a duk duniya in ban da Najeriya da Afghanistan da Pakistan da kuma Chad. Amma a bana, an sake ganin kunnowar cutar a wasu kasashe 4, musamman ma a kasar Somaliya inda fiye da rabin kamuwa da wannan cuta a bana a duniya suke.

Sai dai kuma duk da cewa ana ganin karuwar cutar a wasu sassa na duniya, Lawanson ta ce Najeriya tana kan hanyar kawar da wannan cuta ta Polio a shekarar 2015 idan aka ci gaba da tafiya haka, watau idan cutar ta ci gaba da raguwa haka.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG