Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau talata ma sabuwar tarzoma ta barke a Nigeria a dalilin sakamakon zaben shugaban kasa


Tarzoma ta barke a Kano a bayan zaben shugaban kasa
Tarzoma ta barke a Kano a bayan zaben shugaban kasa

Shedun gani da ido sun bada rahoton cewa an samu barkewar tarzoma a yau talata bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci a kawo karshen boren data barke a saboda hukumar zaben Nigeria ta ayyana cewa shine ya samu nasara.

Shedun gani da ido sun bada rahoto barkewar sabuwar tarzoma a arewacin Nigeria a yau Talata bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci a kawo karshen boren da masu hamaiya suke yi domin nuna rashin amincewa nasarar daya samu. An bada rahoton barkewar tarzoma a kudancin jihar Kaduna musamma a kewayen birnin Kaduna. Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya fadawa Muryar Amirka cewa ma'aikatar kungiyar suna binciken wannan ikirari. A yayinda sojoji ke sintiri a titunan biranen arewacin Nigeria, kungiyar agaji ta Red Cross tace ta dukufa tana aikin ganin ta kaiwa kusan mutane dubu goma sha shidda da suka yi hasarar matsugunin taimakon da suke bukata. Umar Mairiga wanda shine ke lura da harkokin kungiyar ya fadawa Muryar Amirka cewa akwai wadanda suka mutu to amma saura ya rage ga gwamnatin Nigeria ta baiyana yawan mutanen da aka kashe.

Yace an jiwa akalla mutane dari uku da sittin rauni a fafatwar da aka yi. A jiya litinin tarzoma ta barke bayan da aka bada labarin cewa Mr Jonathan ne ya lashe zabe, ya kada Janaral Muhammadu Buhari mai ritaya dan takarar jam'iyar CPC. Yawancin wadanda suka lura da zaben sunce galibi an gudanar da zaben cikin yanci da adalci. A wani jawabin daya gabatar jiya litinin shugaba Jonathan yayi kiran da'a samu hadin kai, yace bai kamata domin an kada wani a zubar da jini ba. Magoya bayan masu hamaiya sunyi ikirarin cewa an tupka magudi a zaben. Babu daya daga cikin jam'iyun masu hamaiya da suka rattaba hannu akan sakamakon zaben na karshe kuma tuni Janaral Buhari ya mika kukar kalubalantar sakamakon zaben a hukunce.

XS
SM
MD
LG