Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kafa Hukumar Rage Radadin Talauci A Najeriya


دنیا کے بیشتر ممالک کے ساتھ برازیل میں بھی چاند گرہن دیکھا گیا۔ برازیل کے دارالحکومت برازیلیا میں چاند گرہن کا ایک منظر.
دنیا کے بیشتر ممالک کے ساتھ برازیل میں بھی چاند گرہن دیکھا گیا۔ برازیل کے دارالحکومت برازیلیا میں چاند گرہن کا ایک منظر.

Majalisar Dattawan Najeriya zata hada gwiwa da Majalisar Wakilai domin a kafa hukumar da za ta rage radaddin talauci a kasar.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amincewa bangaren zartarwa da ta bude wata hukuma ta musamman wadda zata kula da batun talauci da kasar ke fama da ita.

Shugaban kula da harkokin rage radadin talauci a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Mallam Wakili, yace za a rage zafin talaucin ne ta hanyar samarwa da mutane aikin yi. Amma yace da farko sai mutane sun tsarkake zukatansu kafin kawar da mutuwar zuci wanda yayi katutu.

Ganin cewa gwamnatoci da suka shude sunyi irin wannan yunkurin a baya, Mallam Wakikli yace an za a kirkiri ma’aikatar ne domin kyautata kudaden da suke fita, domin sanin ina suka nufa kuma a hannun su waye aka dankawa.

A cewar wata ‘yar Najeriya a Abuja, ba talauci ke damun mutane a Najeriya ba, rashin wadatar zuci ne idan har za a kafa wannan hukuma a saka mutane na kwarai to tabbas zata bayar da goyon bayanta.

Yayin da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ke jin tabakin wasu ‘yan Najeriya, sun bayyana jin dadinsu ga wannan kokari na Majasa, domin suna ganin zai taimaka wajen rage radadin talauci a kasar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG