Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: APC Zata Garzaya Kotu Akan Zaben Taraba


Mukaddashin Gwamnan Taraba na PDP
Mukaddashin Gwamnan Taraba na PDP

Duk da nasarar da jam'iyyar APC ta samu tana zargin an yi mata magudin zabe a jihar Taraba inda ta kuduri aniyar garzayawa kotu.

Jam'iyyar APC da wasu jam'iyyu suna haramar zuwa kotu akan zargin cewa an tafka magudi a wasu wurare a jihar. Zasu kalubali jam'iyyar PDP game da sakamakon zaben.

Jam'iyyun basu amince da samun nasarar PDP ba game da wasu kujerun 'yan majalisar dattawa da na wakilan tarayya.

APC na zargin an yi mata aringizon kuri'u a wasu mazabun jihar. A taron manema labarai da jam'iyyar ta kira shugabanta Alhaji Jika Ardo ya bayyana cewa akwai wurare a Wukari da aka yi magudi. Yace a Wukari an dauko kuri'un ne aka zauna cikin gida ana dangwalasu ba wai mutane ne suka kada kuriun ba. Yace ina ne PDP ta samu mutane dubu sittin da hudu a Wukari.

Kodayake wakilinmu bai samu ya zanta da shugabannin PDP ba saboda wasu dalilai da suka fi karfinsa amma ya zanta da wasu 'yan takarar PDP wadanda suka musanta zargin da APC ke yi. Shehu Marafa Abba da ya lashe kujerar sanata a Taraba ta tsakiya yace kam sun godewa Allah. Ya kira wadanda ya tsaya dasu su yi hakuri domin komi na kan lokaci.

Alhaji Muhammad Danburam daya daga cikin masu sa ido a zaben yace kotu zata yi magani amma kowane dan takara ya tabbatar cewa abun da wakilinsa ya bashi abun da ya gani ne ya kuma gaskanta kana ya yi anfani dashi a kotu.Kada ya je ya bata ma kansa lokaci ya kuma bata lokacin jama'a a kotu. Idan an je a duba zargin kuma babu, to ya yi aikin banza.

Amma Malam Kabiru Jalingo yace a je kotu domin zaben bai yi ba a wasu wuraren. Idan kotu zata yi gaskiya za'a warware matsalolin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG