Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za'a Yi Amfani Da Na'urar Tantance Masu Zabe Ba A Jihar Nija?


Na'urar Karanta PVC.
Na'urar Karanta PVC.

Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Nija tana zargin APC mai mulkin jihar, da shirin magudi a zaben kananan hukumomi da za'a yi ranar Asabar.

Babbar jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Nija, tana zargin ta cewa ta gano wani shirin magudi da jam'iyyar APC mai mulkin jihar take shiryawa, domin ta tafka magudi lokacin zaben kananan hukumomin jihar, wanda za'a yi ranar Asabar mai zuwa 16 ga watan nan na janairu.

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Barista Tanko Beji, yace jam'iyyar ta sami labarin cewa APC ta hukumar zabe ta jihar suna shirin yin aringizon kuri'u ta wajen kin amfani da na'urar tantance masu zabe na kananan hukumomi.

Amma shugaban jam'iyyar APC a jihar Barista Lawal Yusuf, ya karyata wannan zargi, yace bai zo da mamaki ba, jin PDP tana wannan zargi domin babban aikinta shine haddasa rudu da neman tada rigima.

Barista Yusuf, ya bayyana jam'iyyar APC a zaman mai bin doka, wacce taci amfanin na'urar tantance masu zabe, domin haka ba zata amince da duk wani shirin sabanin haka ba.

Amma da yake magana da wakilin Sashen Hausa a yankin Mustapha Nasiru Batsari, kakakin hukumar zabe ta jihar Nija mai zaman kantan, Alhaji Mohammadu Ali, yace babu wata doka data tilastawa hukumar tayi amfani da wadannan na'urorin ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG