Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Zabi Zakarun 'Yan Kwallonku a Afirka


Vincent Enyeama, Victor Moses da John Obi Mikel
Vincent Enyeama, Victor Moses da John Obi Mikel

Yayin da magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Najeria da Burkina Faso ke jiran wasan karshe a gasar kofin nahiyar Afirka na wannan shekara, tagomashin ra'ayin jama'a akan fitattun 'yan wasan nahiyar yayi karin haske akan wadanda ake tunani sun fi fice.

Yayin da magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Najeria da Burkina Faso ke jiran wasan karshe a gasar kofin nahiyar Afirka na wannan shekara, tagomashin ra'ayin jama'a akan fitattun 'yan wasan nahiyar yayi karin haske akan wadanda ake tunani sun fi fice.

Bayan wasanni guda biyu masu kayatarwa tsakanin Najeria da Mali, da Ghana da Burkina Faso, ba magoya bayan kasashen da sukayi nasara bane kawai suke sa ran kallon wasan karshe, har ma da duk mutane a duk fadin duniya saboda kyan kungiyoyin guda biyu.

A wasannin ranar Laraba, Najeria bata yi wa Mali wasa ba, a inda Super Eagles din ta lallasa Mali da ci 4 da 1. Sai dai na Ghana da Burkina Faso bai tafi kamar wasan Najeria ba, saboda kunnen doki ne sakamakon wasan a karshen karin lokaci da aka bayar, amma Ghana ta sha wuya a hannun Burkinan, saboda hare-hare da akayi ta kai mata. A karshe dai, Burkina Faso ce tayi nasara bayan doka fenarity da akayi.

A tagomashin ra'ayin jama'a da Muryar Amurka ke karba domin tantance fitattun 'yan wasa na Afirka, ganin 'yan Najeria masu kuri'u da yawa ba abun mamaki bane, saboda rawar da suka taka a wasannin baya. Mai tsaron gida Vincent Enyeama na da kuri'u 191, John Mikel Obi na da 132, sannan Victor Moses ya samu 135. Amma har yanzu ana iya jefa kuri'a, saboda haka kuri'un zasu canja.

Abun mamaki shine rashin 'yan kwallon Burkina Faso ko guda daya, saboda rashin sanninsu da akayi, sai dai gashi sun doke kasashe masu kyawun 'yan wasa domin fafatawa a wasan karshe.

Za'a rufe jefa kuri'a ranar Lahadi.

A halin da ake ciki dai, Moez Ben Cherifia na Tunisiya ne mai tsaron gidan da yafi sauran na nahiyar Afirka samun kuri'u da guda 221, sannan Seydou Keita na Mali ne zakaran 'yan wasan tsakiya a tagomashin ra'ayin jama'a da kuri’u 213. Fitaccen dan wasan Ivory Coast, Didier Drogba ne a kan gaba a rukunin 'yan wasan gaba da kuri'u 364, sannan da kuri'u 205 ne Souleymane Diawara na Senegal ya zama dodo wajen tsaron baya.

Rabon Najeria da buga wasan karshe a wannan gasa tun shekara ta 2000 a inda kasar Cameroon tayi nasara a bugun fenariti da ci 4 da 3. Sau biyu Najeria tana cin kofin a wasan karshe, a shekara ta 1980 a gida Najeria, da kuma 1994 a Tunisia. Ita kuwa Burkina Faso, bata taba isa wasan karshe ba. Wannan karo shine na farko a tarihi da zata buga wannan wasa.

Za'a doka wasan karshe ran 10 ga Fabrairu a filin wasa na FNB dake birnin Johannesburg.
XS
SM
MD
LG