Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dan Kasar Amurka Daya A Libya A zanga Zanga Kan Wani Silima.


Wannan hoton 'yan Libya suke zanga zanga a Bengazi, kan shugabancin sabbin mahukuntan kasar.
Wannan hoton 'yan Libya suke zanga zanga a Bengazi, kan shugabancin sabbin mahukuntan kasar.
An kashe wani ba Amurke daya, guda kuma aka ji masa rauni lokacinda wani gungun mayakan sakai suka kai hari kan karamin ofishin jakadancin Amurka a Benghazi, lokacin wata zanga-zanga kan wani silima da suka ce ya ci zarafin addinin Islama.

Gungun mutane da suka fusata sun hallara a gaban karamin ofishin jakdancin, suka banka masa wuta.
'Yan kasar Masar suke zanga zangar kyamar soja, kamin a mika mulki ga gwamnatin farar hula ta yanzu.
'Yan kasar Masar suke zanga zangar kyamar soja, kamin a mika mulki ga gwamnatin farar hula ta yanzu.

Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta tabbatar da harin kuma ta ce gwamnati ta hada karfi da ‘yan kasar Libiya domin su tsare ginin. Wata sanarwa ta ce cikin wani lafazi mafi karfi Amurka ta yi tur da Allah wadai da wannan hari da aka kai kan ofishin jakadancin ta.

Haka kuma an yi tarzomar nuna kin jinin Amurka saboda siliman din a kofar ofishin jakadancin Amurka a Alkahira, babban birnin kasar Masar. Wadanda su ka yi zanga-zangar a kasashen duka biyu sun ce siliman din wanda aka yi a Amurka ya ci mutuncin Annabi Muhammad (SAW).
XS
SM
MD
LG