Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZIMBABWE: Ta Na Son Walter Palma Ya Fuskanci Sharia'a a Kasar


Zaki mai suna Cecil da Walter Palma ya kashe a Zimbabwe
Zaki mai suna Cecil da Walter Palma ya kashe a Zimbabwe

Ministan harkokin namun daji na kasar Zimbabwe yace kasarshi na bukatan a mika mata wani dan asalin kasar Amurka da ake zargi da kashe wani sanannen zaki a wani kebabben gandun daji.

Zimbabwe yau Juma’a tayi kira akan a mika wa jami’an gwamnatin ta Walter Palmer, wani likitan hakora dake zaune agarin Eden Prairie Jihar Minnesota a nan Amurka. A halin yanzu Palma ya boye biyo bayan zarginsa da kashe zaki mai suna Cecil a kasar Zimbabwe a farkon wannan wata.

Hukumar kula da namun daji da kifaye yau Alhamis ta bayyana cewa ta fara bincike akan kashe zakin, kuma bata samu nasarar ganawa da Palmer ba. Hukumar ta yi kira ga Palmer ko wakilansa akan su tuntubi jami’an gwamnatin Amurka nan take.

Ta kuma kira kashe zaki Cecil abun takaici, sannan ta kara da cewa zata yi kokarin kwakulo gaskiyar abunda ya faru a bincike da zata gudanar.

Wani shaida dake kusa da binciken ya bayyanawa jaridar Reuters cewa hukumar kula da namun dajin na gudanar da bincikenta ne a karkashin wata dokar Amurka mai suna Lacey Act, wadda ta hana ciniki da safarar namun daji wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. Binciken ya mayar da hankali ne akan ko akwai hannun Palmer a yunkurin karya doka.

A halin da ake ciki kuma fadar shugaban Amurka ta White House tace zata duba bukatun jama’a da aka fi sani da Petition a turance, na mikawa hukumomin Zimbabwe mutumin da ya kashe Cecil.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG