Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Duniya ya bukaci gwamnatocin kasashen Afrika su kara kaimi a yaki da HIV


Wani yana fama da cutar HIV
Wani yana fama da cutar HIV

Bankin Duniya ya bukaci gwamnatocin Afrika su kara kaimi a shawo kan kamuwa da HIV

Babban Bankin Duniya ya yi kira ga gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika su kara kaimi wajen hana al’ummarsu ci gaba da kamuwa da cutar kanjamau.

Babban Bankin Duniyan ya bayyana cewa, idan ba a dauki kwararan matakai ba, shawo kan cutar zai zama da wuya sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar.

Bankin ya kwatanta yaki da cutar shan inna da masu karbar kudin fansho, inda a kullum ake samun Karin wadanda suke shiga tsarin. Ya kuma shawarci gwamnatoci su kara kaimi wajen shawo kan yaduwar cutar.

An sami Karin tallafin kudin da ake bayarwa a yaki da cutar kanjamau daga dala miliyan 260 a shekara ta 1996 zuwa biliyan 15 a shekara ta 2010. Sai dai babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga masu bada tallafi su kara bada gudummuwa domin cimma burin tara kimanin dala biliyan 24 da aka kiyasta kashewa a shekara domin yaki da cutar HIV.

Kasashen nahiyar Afrika sun ci gaba da kasancewa inda ake fama da cutar duk da yake nahiyar tana da kashi 12% ne kawai na adadin al’ummar duniya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG