Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun Jarin Bankin Standard Chartered Na Ingila Yayi Kasa Saboda Zargin Hulda Da Iran.


Masu zanga zanga a birnin New York.
Masu zanga zanga a birnin New York.
Hannun jarin Bankin Standard Charted na Ingila yayi kasa, a hada-hadar ranar talata, kwana daya bayanda jami’an amurka suka yi zargin Bankin da badda sawun kudade dala milyan dubu $250 a hulda da kafofin kudi na Iran cikin shekaru 10 da suka wuce.
Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron. (file photo)
Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron. (file photo)

Bankin wanda shine na biyar a girma a Ingila, yana da rassa masu yawa a sassan duniya da dama, kawo yanzu ba a taba shi a irin abin fallasa da ya taba Bankunan Ingila ba. Amma babban mai sa ido kan harkoin Banki a New York, yayi zargin cewa Satandard Chartered cikin shekaru daga 2001-zuwa 2010 da suka wuce, yana ta gaban kansa ba tareda bin ka’idoji ba.

Babban jami’in sa idon yace Bankin ya sami daruruwan miliyoyin dala ta wajen tace kudade daga hukumomin Iran har sau kusan dubu sittin. Wadannan hulda inji jami’in ya buda Bankunan Amurka ga ‘yan ta’adda, masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma kasashe da ake yiwa kallon basu da mutunci.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) ya fara binciken gano kan an aikata laifi.

Wani mai fashin baki kan harkokin Bankuna Amurka Bert Ely ya gayawa Muriyar Amurka cewa binciken da ake gudanarwa bangare nan a kokarin Amurka da kwayenta na yammacin duniya suke yin a dakatar da shirin Nukiliyar Iran,zargi da Iran take musantawa.
XS
SM
MD
LG