Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jakadan Amurka A Kasar Libya


Wani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar Libya
Wani dan zanga-zanga a kofar karamin ofishin jakadancin Amurka dake cin wuta a Benghazi a kasar Libya

An kashe jakada Chris Stevens tare da wasu jami'an jakadanci uku a farmakin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi

An kashe jakadan Amurka a kasar Libya tare da wasu ma’aikatan jakadanci guda uku, a bayan da gungun mutane suka abka cikin karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Benghazi na gabashin kasar jiya talata da maraice.

‘Yan zanga-zangar da aka ce sun fusata da wani fim na batunci ga Annabi Muhammad (saw) wanda wani mutumin da ba kwararre ba ya hada shi a nan Amurka, sun yi harbi a kan karamin ofishin jakadancin na Amurka dake Benghazi, suka kuma cinna masa wuta.

Jakada J. Christopher Stevens shi ne jakadan Amurka na farko da aka kashe a wata kasar waje a cikin shekaru fiye da 20. Shi kwararre ne a fannin huldar Amurka da kasashen waje, kuma yana daya daga cikin jakadun Amurka da suka fi kwarewa kan harkokin wannan yanki. A cikin watan Mayu ya kama aiki a birnin Tripoli.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da rahoton cewa jami’in kula da harkokin yada labarai Sean Smith na cikin wadanda aka kashe. Sakatriyar harkokin waje Hillary Clinton ta ce har yanzu su na kokarin sanar da iyalan sauran jami’an guda biyu kafin a bayyana sunayensu.

A yau laraba, shugaba Barack Obama yayi Allah wadarai da kisan Amurkawan su hudu.

Shugaban ya fada a cikin wata sanarwa cewa mutanen hudu, misali ne na kudurin Amurka na wanzar da ‘yancin walwala, da adalci da kuma kawance da kasashe tare da jama’a a fadin duniya,l yana mai fadin cewa, rayuwarsu ta sha bambam, a fili, da irin ta mutanen da suka hallaka su.

Shi ma mukaddashin firayim ministan Libya, Mustafa Abu Shagour, yayi Allah wadarai da kisan jami’an jakadancin hudu na Amurka, yana mai bayyana wannan a zaman aiki na ragwanci.

‘Yan tawayen kasar Libya su na kaunar Stevens sosai a sabvoda irin goyon bayan da ya bayar ga tunzurin da suka yi har suka kawar da shugaba Muammar Gaddafi daga kan mulki.
XS
SM
MD
LG