Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin JTF Da Boko Haram Ya Kaure A Potiskum


Sojoji su na wucewa ta jikin wasu gidajen da aka kona a Maiduguri, 8 Oktoba, 2012
Sojoji su na wucewa ta jikin wasu gidajen da aka kona a Maiduguri, 8 Oktoba, 2012

An yi ta jin fashe-fashe da harbe-harbe tun daga karfe 6 na safiyar yau laraba a garin na Potiskum dake Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya

Fashe-fashe da kuma karar harbe-harbe sun jijjiga wani gari yau laraba a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kwana biyu bayan da aka kashe mutane 24 a wani tashin hankali a wannan yanki.

Mazauna garin Potiskum a Jihar Yobe, sun ce an fara gwabzawa da misalin karfe 6 na safe. Wani gidan telebijin mai suna Channels TV yace dakarun tsaron Najeriya su na gwabzawa ne da ‘ya’yan kungiyar na ta Boko Haram.

Rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF ta fada cewa a ranar litinin da maraice ta kashe ‘yan Boko Haram su 24 ta kuma kama makamai masu yawa a birnin Maiduguri. Wata sanarwa ta ce ‘yan Boko Haram din su na buya a cikin gidajen fararen hula domin kai farmaki a kan dakarun JTF.

Shaidu sun zargi rundunar JTF da laifin cin zarafin jama’a a fadan da take yi da ‘yan Boko Haram. A makon jiya, rundunar ta musanta zargin cewa sojoji sun kashe mutane akalla 30, suka kona kantuna da gidajen jama’a a Maiduguri, a wani matakin daukar fansar wani harin bam da aka kai musu.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta fada a makon jiya cewa da alamun dukkan bangarorin sun aikata laifuffuka na cin zarafin bil Adama.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG